Recent Posts

header ads

Na Fi Son Yin Soyayya Da Saurayi Mai Duka Na – Inji Wata Jarumar Fim


Jarumar masana’antar fina-finai na kasar Tanzania, Wema Sepetu, ta bayyana cewa ta fi son soyayya da saurayi ko miji wanda zai rinka dukanta.

Kyakkyawar ‘yar wasar kwaikwaiyon ta kasance ita ce ta lashe gasar mace wacce ta fi kowace mace kyau a kasar Tanzania a shekarar 2006.

Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da ta halarci taron murnar ranar haihuwar manajanta, Neema Ndepanya, a Salasala, Dar es Salam.

A nan ne ta fadawa kafafen yada labarai na Ijumaa Wikeinda cewa tana fi son yin soyayya da saurayi ko miji mai dukan ta a kai a kai a duk lokacin da ta yi abu ab dade ba.

“Ina son saurayi ma duka na a kai a kai, ba wanda za mu dade tare da shi ba ba tare da ya sa mun hannu ba, ko dan mari ne” ta ce sannan ta fashe da dariya.

Post a Comment

0 Comments