Recent Posts

header ads

Domin Matasa: Kalar Auren Da Na Ke Muradi


Matasa wannan sashe ne na musamman da muka kirkiro muku domin bayyana irin auren da mutum yake da muradin yi. Za a iya aiko mana da bayani dalla-dalla kan irin auren da ake matukar son yi tun daga kan irin yarinyar da kake so ka aura ko irin saurayin da kike so ki aura har zuwa yanayin bikin da za a yi da kuma uw-uwaba zamantakewar da mutum yake fatan yi da iyalinsa daga lokacin da aka daura ma sa aure. A aiko ta adireshinmu na email: leadershipayaujumaa@gmail.com ko kuma a tuntube mu ta 08034980391.

Yanzu ga somin-tabi daga Yusuf Dankwalisa:

Ni dai sunana Yusuf Shuaibu auren da na ke muradi, shi ne kamar haka; na farko dai ina bukatar mace doguwa sannan kuma fara mai halaye kamar haka, tarbiya, gimama na gaba da ita, addini da kuma iya soyayya.

A bangare daya kuma, irin zaman da na ke so mu yi da ita kuma shi ne, zama na amana, mutunta juna, kiyaye hakkin juna, tausaya wa juna, mutunta iyayen juna da kuma yaw a juna idan aka yi abin da ya dace.

Idan kuma Allah ya a zurtamu da haihuwa, ina son karta dauki soyayyata ta bawa yaron da muka haifa gaba daya, wato ina nufin ta dai ba yaran dai-dai bakin gwargwado ni kuma ta bani nawa nawa soyayyan ba tare da ta rage ba.

Domin mafiya yawan ma’aurata idan suka haifu sai ka ga sun dauki soyayya gaba daya sun bawa yara yayin da shi kuma maigida sun bar shi da kallon sama. Irin wannan zama ya kan iya jawo nakasu ga zamantakewan ma’aurata, ni kuma san bana sha’awar hakan a cikin zamantakewar aure na.

Source Leadership Hausa

Post a Comment

0 Comments